Kungiyar ta bayyana haka ne a jiya laraba ta kuma bukaci gwamnatin Nigeria ta mutunta hukuncin babban kotu a kasar na sakin malamin da kuma biyansa diyya da shi da matarsa.
Mr Mausi Segun, babban mai bincike a cikin kungiyar ya kara da cewa akwai bukatar gwamnatin tarayyar kasar ta hukunta duk wadanda suke da hannu a cikin kissan yayan wannan kungiyar a cikin watan Decemban shekarar da ta gabata sannan ta bada umurnin a dakatar da takurawa yan kungiyar.
Kungiyar human Right watch dai ta kammala ta cewa ta dau wannan matakin na kiran gwamnatin Nigeria ta sake malamin ne bayan da rahoton kimitin binciken da gwamnatin jihar kaduna ta kama ta tabbatar da hannu da kuma laifin jami'an tsaro kan kisan kiyashin da aka yiwa yayan wannan kungiyar a ranar 12-14 ga watan Decemban bara.
A cikin watan da ya gabata ne gwamnatin jihar Kaduna a arewacin kasar ta sha alwashin gurfanar da shugaban kungiyar ta IMN kan zargin take doka wanda kungiyarsa ta yi ta yi a cikin shekaru kimani 30 da suka gabata. 288